Ana gwabza yaki a Syria | BBC news

AFP

Hakkin mallakar hoto
AFP

Ana gwabza yaki kusa da garin Ras al-Ain na Syria da ke kan iyakar kasar tsakanin mayakan Kurdawa da kuma sojojin Turkiyya.

Turkiyya ta bayyana cewa ta kwace iko da garin amma mayakan Kurdawa na SDF sun musanta hakan.

Kasar ta Turkiyya ta musanta kai hari ga sojojin Amurka bayan shelkwatar tsaron Amurkar ta bayyana cewa an kai hari ga dakarunta da ke yammaci.

Rahotanni sun bayyana cewa a kalla an kashe fararen hula 30 kuma sama da mutum 200,000 sun rasa muhallansu a cikin kwanaki hudu.

Matakin da Shugaba Trump ya dauka na janye dakarun Amurka daga yankin ya yi sanadiyar kara harzuka harin da Turkiyya ta kai wa mayakan Kurdawa.

Turkiyyar dai ta zargi Kurdawa da ”ta’addanci” inda ta ce tana so ta tasa keyarsu daga inda take so ta kafa sansaninta a cikin Syria domin shirinta na tsugunar da ‘yan gudun hijirar Turkiyya a kasar kusan miliyan uku.

Mayakan Kurdawa na cikin kawayen Amurka na yaki da ‘yan kungiyar IS.

Wani babban kalubale da kasashen duniya ke fuskanta shi ne makomar dubban fursunonin yaki na kungiyar IS da suke hannun mayakan Kurdawa da ke yankin.

A cikin makon nan dai Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoto inda ta bayyana cewa a kalla mutane 100,000 ne suka yi kaura daga gidajensu a arewacin Syria sakamakon hare-haren Turkiyya a yankunan da ke hannun mayakan Kurdawa.

Rahotannin Majalisar Dinkin Duniya sun ce mutanen na zama ne a makarantu da wasu gine-gine.

Related Articles