A yanzu haka dai dimbin masu zanga-zanga na gudanar da zanga-zanga kan wata babbar hanya a garin Kugbo da ke Asokoro a karamar hukumar Abuja Municipal Council (AMAC).
Masu zanga-zangar wadanda suka fito a daruruwansu sun ki ja da baya duk da harbin bindiga da hayaki mai sa hawaye da jami’an tsaro suka jefa musu.
Idan ba a manta ba, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana masu zanga-zanga zuwa filin wasa na Moshood Abiola.
Amma yayin da wasu daga cikinsu suka zarce zuwa filin wasan, wasu kuma sun taru a wurare daban-daban na babban birnin kasar.
Jami’an tsaro dai na cikin tsaka mai wuya wajen shawo kan gungun matasa da ke dagewa cewa za su ci gaba da zama a kan tituna har sai an biya musu bukatunsu na inganta tattalin arziki.
Asokoro, inda masu zanga-zangar suke, ya kunshi kujerar mulkin Najeriya, cibiyoyin gwamnati, barikokin soji da kuma babban ofishin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).