Ana fargabar mutuwar mutane da dama gobarar tankar iskar gas a Abuja

Wata tankar iskar gas ta yi bindiga ta fashe ta kuma kama da wuta  a gadar Karu dake kan babbar hanyar  Abuja-Keffi.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba inda ya rutsa da ababen hawa da dama abun da yasa wasu ke fargabar cewa wutar da ta tashi ta rutsa da mutane da dama.

Har ila yau ya janyo cunkoson ababen hawa akan titin da ako da yaushe yake da yawan motoci dake zirga-zirga.

Wata da ta sheda faruwar lamarin ta faɗawa jaridar Daily Trust cewa abun ya faru cikin sauri kamar ƙiftawar ido.

“Ni da kaina na ƙirga motoci biyar  da suka ƙone amma na naji ance sama da motoci 20 abun ya shafa,” a cewarta.

More from this stream

Recomended