Ƴan bindiga sun kai farmaki ƙaramar hukumar Ehime-Mbono ta jihar Imo a ranar Talata inda suka kashe dakarun sojan Najeriya a wani sansaninsu dake yankin.
Harin na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da wasu ƴan bindiga suka ƙona ginin jami’ar karatu daga gida wato National Open University Of Nigeria dake ƙauyen Ezeoke-Nsu dake ƙaramar hukumar ta Ehime-Mbono.
Maharan sun kuma ƙona gidan Frank Ibezim wani tsohon sanata Ahmed da ya taɓa wakiltar al’ummar yankin mazaɓar Imo ta arewa.
Wani fefan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwar zamani ya nuna ƴan bindigar suna rera waƙoƙin yaƙi dai-dai lokacin da suke kunnawa gine-ginen wuta.
Wani mazaunin garin da abun ya faru ya ce maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 08:30 na daren ranar Talata.
Henry Okoye mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce rundunar bata samu bayani ba kan faruwar lamarin.