Ana fargabar mutuwar mutane a harin ƴan bindiga kan sojoji a jihar Imo

Ƴan bindiga sun kai farmaki ƙaramar hukumar Ehime-Mbono ta jihar Imo a ranar Talata inda suka kashe dakarun sojan Najeriya a wani sansaninsu dake yankin.

Harin na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da wasu ƴan bindiga suka ƙona ginin jami’ar karatu daga gida wato National Open University Of Nigeria dake ƙauyen Ezeoke-Nsu dake ƙaramar hukumar ta Ehime-Mbono.

Maharan sun kuma ƙona gidan Frank Ibezim wani tsohon sanata Ahmed da ya taɓa wakiltar al’ummar yankin mazaɓar Imo ta arewa.

Wani fefan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwar zamani ya nuna ƴan bindigar suna rera waƙoƙin yaƙi dai-dai lokacin da suke kunnawa gine-ginen wuta.

Wani mazaunin garin da abun ya faru ya ce maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 08:30 na daren ranar Talata.

Henry Okoye mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce rundunar bata samu bayani ba kan faruwar lamarin.

More News

Magoya bayan jam’iyar NNPP sun ƙona jar hula

Wasu daga cikin mambobin wani tsagi na jam'iyar NNPP sun barranta kansu da jagoran jam'iyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso inda suka riƙa...

Magoya bayan jam’iyar NNPP sun ƙona jar hula

Wasu daga cikin mambobin wani tsagi na jam'iyar NNPP sun barranta kansu da jagoran jam'iyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso inda suka riƙa...

PDP ta ɗauki hanyar warware rikicin jam’iyar

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ce  an kawo karshen rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami'yar PDP. Mohammed wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin...

Dakarun Najeriya sun cafke wasu ƴan’aiken ƴanbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...