Ana duba yiyuwar kai shugaban kungiyar ƙwadago ta NLC asibitin kasar waje

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta ce tana tattaunawa kan duba yiyuwar kai shugaban kungiyar Joe Ajaero ƙasar waje domin a duba lafiyarsa.

Benson Upa mai magana da yawun kungiyar shi ne ya bayyana haka ranar Alhamis inda yace kungiyar na duba yiyuwar hakan ne saboda ya nayin raunukan da shugaban yaji a jihar Imo ranar Laraba.

A ranar Laraba aka bada rahoton cewa wasu jami’an tsaro sun yi awon gaba da Ajaero a hedikwatar kungiyar ta NLC dake jihar Imo.

Kungiyar ta NLc ta ce an rufe idon Ajaero tare da lakaɗa masa duka bayan da jami’an tsaro suka kama shi.

NLC ta ce an kai shugaban cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Owerri domin samun kulawar likitoci.

Da take musalta kamen hukumar yan sandan jihar ta ce ta ɗauke shugaban kungiyar ta NLC ne domin hana wasu batagarin matasa yi masa duka.

A makon da ya wuce ne kungiyar NLC tayi barazanar tsayar da ayyuka a jihar saboda yadda gwamnan jihar Hope Uzodimma ya gaza biyan ma’aikatan jihar hakkinsu.

More from this stream

Recomended