Ana cigaba da zaman d’ar-d’ar a Jos yayin da ake fargabar mutuwar mutane da dama

Mutane da yawa ne ake fargabar sun mutu a wajen titin Rukuba dake kusa da birnin Jos bayan da wani hari da aka kai da daddare ya jawo harin ramuwar gayya kan mutanen da basu ji ba su gani ba da safiyar ranar Juma’a.

Wata majiya ta shedawa jaridar Daily Trust cewa wasu yan bindiga ne suka kai hari yankin da daddare inda suka kashe akalla mutane 10.

Matasa dake yankin sun shiga kai harin ramuwar fansa akan masu motoci matafiya.

Ya zuwa yanzu dai ba a iya tantance mutane nawa rikicin ya rutsa da su amma kwamandan rundunar samar da tsaro dake jihar ta ‘Operation Safe Haven’ Manjo Adam Umar da kuma kakakin rundunar ƴansandan jihar, Tyopev Terna sun tabbatar da cewa dakarun tsaro sun isa wurin.

Wakilin jaridar ta Daily Trust ya lura cewa shaguna da dama sun rufe mutane na cigaba da al’amuransu na yau da kullum a birnin.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...