Gwamnatin tarayya ta sanar da kamfanonin jirage 4 a matsayin wanda za su ɗauki alhazan Najeriya a aikin hajjin shekarar 2025.
Shugaban hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa NAHCON, Abdullahi Usman shi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar a Abuja.
Kamfanonin Jiragen da za su yi aikin jigilar alhazan sun haɗa da Air Peace, Fly Nas, Max Air da kuma Umza Air Services.
Shugaban ya ce an zaɓi kamfanoni huɗun ne cikin 11 da suka nemi a basu damar ɗaukar alhazan Najeriya ya zuwa Saudiyya..
Ya ƙara da cewa wani kwamiti mai mambobi 32 ne aka ɗorawa alhakin tantancewa tare da zaɓen kamfanonin da za su yi aikin jigilar.
Har ila yau hukumar ta zaɓi wasu kamfanoni uku da za su yi aikin dakon kayan alhaza.
Kamfanonin sun haɗa da Aglow Aviation Support Services Ltd, Cargozeal Technology Ltd., da kuma Qualla Investment Ltd.