An yi zanga-zanga a fadar shugaban ƙasa da majalisar ƙasa kan dawo da Sarki Sanusi

Wasu masu zanga-zanga sun yi jerin gwano ya zuwa ƙofar fadar shugaban ƙasa da kuma majalisar dokokin ta tarayya kan dawo da Sarki Muhammadu Sanusi kan karagar mulkin jihar Kano.

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da dawo da  Sanusi a matsayin Sarkin Kano bayan da ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautu ta jihar.

Majalisar dokokin jihar Kano ce tayi gyara kan dokar da tam ta raba masarautun jihar zuwa biyar ta kuma sauke Sanusi daga kujerarsa.

Duk da cewa wata kotu a jihar Kano ta bayar da umarnin cewa kada gwamnatin Kano ta aiwatar da kudirin dokar tuni gwamnatin ta yi gaban kanta ta naɗa Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16  a daular fulani.

Da yake magana da manema labarai a yayin zanga-zangar ranar Juma’a, Abdullahi Saleh jami’in tsare-tsare na ƙungiyar Northern Nigeria Peace and Development Foundation ya ce gwamna Yusuf ya ɗauki matakin ne domin batawa wanda ya gada wato tsohon gwamna Ganduje.

Saleh ya ce ya kamata shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanya baki domin gudun karyewar doka da oda.

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa ɗansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...