An yi taron addu’a a Jigawa kan rashin tsaro da matsin rayuwa

Wata kungiyar jin Æ™ai mai suna Sawaba Humanitarian Initiative ta gudanar taron addu’a na musamman domin kawo Æ™arshen matsalar tsaro da tattalin arziki dake wahalar da Æ´an Najeriya.

An gudanar da taron addu’ar ne a Dutse babban birnin jihar Jigawa bayan da duk Æ™oÆ™arin da jami’an tsaro suka yi na hana taron ya ci tura.

Daruwan-ÆŠaruwan mutane da suka halarci taron addu’ar sun bayyana damuwarsu kan makomar Æ™asarnan dai-dai  lokacin da yunwa, cututtuka da talauci ke cigaba da kashe mutane a kullum a yayin da waÉ—anda suke kan mulki a ke cigaba da nuna ko-in-kula kan halin da ake ciki.

Da yake magana bayan taron addu’ar, shugaban Æ™ungiyar Sawaba Humanitarian Initiative na Æ™asa, Kwamared Umar ÆŠanjani Hadejia ya ce halin da ake ciki na nema yafi Æ™arfin talaka.

“Sai da na kasa riÆ™e hawaye bayan da naga yadda yunwa take wahalar da tsofaffi da yara ar Æ™auyukan Jigawa,”

“Babu É—an siyasa mai hankali da zai yi bacci lafiya bayan ganin abun da na gani a Æ™auyuka da dama,” ya ce .

Ya ce za gudanar da irin wannan addu’ar a Æ™ananan hukumomin jihar.

More News

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da Æ´an ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an Æ´an sanda da kuma sojoji suna É—aukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar Æ´an sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...

Sojoji sun kashe É—an Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya na Birged Ta 21 dake aiki da rundunar Operationa HaÉ—in Kai dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso...