An yi ruwa da iska mai tsanani a Makkah

[ad_1]

Hakkin mallakar hoto
Shaykh Mohammed Aslam

An yi iska mai karfi da guguwa da kuma ruwan sama da aka dauki lokaci ana yi yayin da alhazzan ke shirin fita filin Mina da ke wajen garin Makka, inda daga nan suke wuce wa zuwa filin Arafat.

Hukumar kula da yanayi ta Saudiyya ta yi hasashen cewa za a yi matsanancin zafi a ranar Litinin da ake hawan Arafat, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Jaridar ta ce hasashen ofishin kula da yanayi na Saudiya ya nuna sai zuwa yammacin Litinin za a yi iska da kura da kuma ruwan sama a Makkah saboda matsanancin zafin da aka maka.

Bisa ga bayanin da Hukumar Gudanar da Harkokin Kiwon Lafiyar Harkokin Kiwon Lafiyar Kwayoyi da Tsarin Tsarin Harkokin Kiwon Lafiya ke yi, ruwan sama da ruwan sama na iya kaiwa wurare masu tsarki da Makka har sai daren Litinin.

Rahotanni sun ce yanayin zafin ya kai maki 43, kuma hukumomin saudiya sun ce yanayin zai karu da kusan kasha 65.

Wani ya wallafa bidiyo a shafin facebook yana mai cewa an yi iska da ruwan sama a Makkah da Arafat da Mina da kuma Muzdalifah.

Iska da aka yi dai ta lalata wasu runfunan alhazzai a Mina, yayin da aka bukaci alhazzai su kiyayen umurni da shawarwarin da hukumomi suka bayar kan yanayin.

Musulmai kimanin miliyan biyu da ke gudanar da aikin hajji suke tsayuwar Arfa ranar Litinin, kololuwar ibadar aikin hajji.

Tun da farko hukumomin Saudiyya sun ce sun zamanantar da kayayyaki da gine-gine don karbar alhazai.

Daga cikin sabbin abubuwan da hukumomin suka bullo da su har da manhajojin wayar salula na fassara yaruka da neman taimakon likita da sauran bukatun mahajjata.

Mahajjatan dai za su shafe wuni suna addu`o`i da karatun alkur`ani, har zuwa faduwar rana inda daga za su wuce Muzdalifah su kwana a sarari.

Malaman addinin Islama sun bayyana ranar Arafah a matsayin ranar da tafi muhimmanci a cikin ranakun shekara a addinin Musulunci.

Sheikh Muhammad Tukur Almannar, wani malamin addinin muslunci a Kaduna a Najeriya ya ce wannan rana ce da Allah ke gafarta wa dukkanin al’ummar musulmin da suka halarci wajen Arafah.

Ya kuma ce rana ce da Iblis wato shedan ya fi kaskanta da wulakanta saboda hassada da rashin jin dadin gafartawa dukkanin al’ummar da suke a wajen Arafah.

Sheikh Almannar ya ce daga cikin irin ayyuka kuma da suka kamata Musulmi su yi domin samun amfanin wannan rana, sun hada da yin azumi, ga wadanda ba su samu damar zuwa aikin Hajjin ba.

[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...