An yi hasarar rayuka a wani hatsarin jirgin ruwa a Najeriya

An tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da ceto wasu 30 a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Kogin Niger da ke kusa da Mmiata Anam a karamar hukumar Anambra ta Yamma a jihar Anambra.

An tattaro cewa kwale-kwalen yana tafiya ne daga jihar Kogi zuwa Anambra ta kogin Niger kafin ya kife a gabar kogin Mmiata.

Wata majiya a yankin Riverine na al’ummar ta shaida cewa lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi.

Wani faifan bidiyo da aka yi ya nuna cewa waɗanda suka mutu mata ne da yara.

More from this stream

Recomended