Ƴan bindiga sun yi garkuwa da, Chiamaka Obi wata mai yiwa ƙasa hidima wato NYSC a jihar Niger akan hanyarta ta zuwa jihar Imo.
Obi wacce ta fito ne daga ƙauyen Edenta na garin Okwu Etiti a ƙaramar hukumar Orsu ta jihar Imo an kuma yi garkuwa da ita ne a ranar Litinin lokacin da take dawowa daga jihar Kebbi bayan da ta kammala aikin yiwa ƙasa hidima a can.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa anyi garkuwa da ita ne tare da wasu iyalai su huɗu, direban motar da kuma wasu fasinjoji uku.
Da yake tsokaci kan batun, Uche Agabige ɗan majalisar dokokin jihar Imo ya ce masu garkuwar sun buƙaci biya su maƙudan kuɗi kafin su sake ta.
Agabige ya bayyana damuwarsa kan halin da Obi ta ke ciki a yayin da ya shawarci gwamnatin jihar Imo da ta kaddamar da bincike kan garkuwar da da aka yi da ita.
Ɗan majalisar ya kuma shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya kawo ƙarshen yin garkuwa da mutane a Najeriya