An yi garkuwa da masu hakar ma’adanai 16 a jihar Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna a ranar Laraba ta tabbatar da anyi garkuwa da wasu masu hakar ma’adinai a kauyen Bogoma a karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar,Yakubu Sabo shine ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN haka a Kaduna.

Sabo ya ce masu hakar ma’adanan su 16 an sace su ne dai-dai lokacin da suke komawa gida cikin wata babbar mota daga wurin da suke hakar ma’adanan.

“Barayin sun kama wani mai suna Isa Sa’idu da kuma wasu mutane 15 dukkaninsu sun fito daga kauye ɗaya,” ya ce.

Ya kara da cewa tawagar rundunar ƴansanda ta musamman dake yaƙi da garkuwa da mutane na bincika yankin domin ganin an ceto mutanen tare da kama masu garkuwa da su.

Aikata garkuwa da mutane a yankin na birnin Gwari a bune da ya zama ruwan dare a yankin duk da kokarin da hukumomin tsaro suka ce suna yi na shawo kan lamarin.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...