An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke Abuja, biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin sojoji da wasu ‘yan kasuwa a ranar Asabar.

Wani faifan bidiyo da manema labarai suka gani a ranar Asabar ya nuna dimbin fararen hular da suka yi galaba a kan wasu sojoji yayin wani artabu da suka yi a Banex.

Hedkwatar tsaro, da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ba a samu damar jin ta bakinsu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

A halin da ake ciki, wani dan kasuwa da ya bayyana sunansa da Abdul, ya shaida wa ƴan jarida a ranar Asabar  cewa rikicin ya barke ne a kan sayar da wayar salula.


Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ce kwamishinan ‘yan sandan, Benett Igweh ya tura jami’an hukumar bayar da taimakon gaggawa

Adeh ta tabbatar da cewa “CP ta tura tawagar sirri zuwa wurin.”

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...