An yanke wa matashi hukuncin kisa a Zamfara

Wata babbar kotun jihar Zamfara ta yanke wa wani Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe abokinsa saboda naira 100.

An gurfanar da Dahiru a kotu ne a watan Yunin 2017 bisa zarginsa da kashe abokinsa, Shamu Ibrahim, da wuka har lahira a lokacin da suke ke fada da juna saboda kudi N100.

Da yake karanta hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a Mukhtar Yusha’u, ya ce wanda ake zargin Anas Dahiru da ke Unguwar Dallatu da ke Gusau babban birnin jihar, an gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2017 bisa zargin kashe abokinsa, Shamsu Ibrahim, tare da kashe shi.

Yusha’u ya ce bayan ya saurari bangarorin biyu, ya yanke wa Anas hukuncin kisa bisa laifin kashe abokin nasa.

Ya ce, “Bayan ya saurari bangarorin biyu, na yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wanda ake tuhuma (Anas Dahiru) kamar yadda ya zo a sashe na 221 na kundin Code. .”

More News

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...

Daurawa ya yi murabus daga muƙamin shugabancin Hisbah a Kano

Sheikh Aminu Daurawa ya yi murabus daga muƙaminsa na Shugaban Hisbah na Jihar Kano. Malamin yace ya yi iya kokarinsa wajen gyaran tarbiyar matasan Kano...

Tirkashi: Matashi ya yi tattaki tun daga Gombe har Abuja

Wani direban mota mai shekaru 21 daga jihar Gombe, Suleiman Rabiu, ya yi tattakin sama da kilomita 700 domin nuna yabonsa ga Hafsan Hafsoshin...