
Wani yaro mai shekaru biyar da aka bayyana da suna Salmanu aka bada rahoton gano shi cikin jini bayan da aka yanka wuyansa a wani kauye dake karamar hukumar Kazaure ta jihar Jigawa.
Bayanan da suka fito daga garin na nuni da cewa yaron ya mutu a asibiti inda aka garzaya da shi sakamakon zubar da jini da yayi da yawa.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu shi ne ya tabattar da faruwar lamarin.
Ya kuma kara da cewa an samu wasu yan bindiga da suka sace mahaifin, Hon Sale Baba Buji dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Buji a majalisar dokokin jihar.