Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta gano gawar wani mutum da aka sace a Abuja, inda aka tsinci shi da raunukan harbi a jikinsa a kan titin Kabode da ke cikin Karamar Hukumar Kachia ta jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa gawar mutumin ta bayyana ne a ranar 21 ga Oktoba bayan dagacin ƙauyen Iseme Kachia, Halilu Ayuba, ya kai rahoto ga hukumomi.
Wani mazaunin yankin mai suna Jamilu Danazumi daga ƙauyen Kabode shi ne ya gano gawar da misalin ƙarfe 12 na rana, yayin da yake kan hanyar zuwa Kachia. An gano cewa mutumin ya samu harbin bindiga a ƙirji kuma an same shi a kusa da sansanin horon sojoji na Nigerian Army Exercise Camp da ke kan titin Kabode.
‘Yan sanda sun bayyana cewa an samu takardar da ke ɗauke da lambobin waya guda biyu a aljihu na mamacin. Da aka kira lambobin, an gano cewa na danginsa ne, kuma sun tabbatar da cewa an sace mutumin ne tun ranar 2 ga Oktoba a ƙauyen Bukwa da ke Abuja.
An Tsinci Gawar Mutumin Da Aka Sace A Abuja A Jihar Kaduna
