An sanar da kuɗin kujerar aikin hajji

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa NAHCON ta sanar da kudin kujerar aikin hajjin shekarar 2025.

A wata sanarwa ranar Litinin mai magana da yawun hukumar , Fatima Sanda Usara  ta ce kuɗin da maniyata daga jihar Borno da Adamawa za su biya zai kama naira miliyan N8,327,125.59 a yayin da sauran maniyata suka fito daga sauran  jihohin arewa za su biyaN8,457,685.59.

A  cewar sanarwar maniyatan da suka fito daga jihohin kudu za su biya N8,784,085.59.

An cimma matsaya ne kan kuɗin kujerar aikin hajjin bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan aikin hajjin.

Ta ƙara da cewa shugaban hukumar aikin hajjin ta ƙasa, Abdullahi Saleh da kuma shugabancin kungiyar shugabannin hukumomin aikin hajji na jihohi sun yi aiki tukuru wajen ganin ba a samu kari ba a kudin kujerar aikin hajjin na bana.

More from this stream

Recomended