An kaure da hayaniya a yayin zaman majalisar wakilai na ranar Alhamis bayan da ɗan majalisar wakilai daga jihar Filato, Ajang Iliya ya sauya sheƙa daga jam’iyar Labour Party ya zuwa jam’iyar APC.
Tajuddeen Abbas kakakin majalisar shi ne ya karanta takardar sauya shekar ta Iliya wanda ya ke wakiltar al’ummar ƙananan hukumomin Jos South da Jos East a majalisar .
Iliya ya bayyana rikicin shugabanci da ake fama da shi a jam’iyarsa ta LP a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyar.
Duk da cewa tuni hukuncin kotu ya tabbatar da Julius Abure a matsayin halastaccen shugaban jam’iyar ta LP har yanzu kwamitin shugabancin riƙo na jam’iyar a ƙarƙashin jagorancin Esther Nenadi Usman na cigaba da ikirarin jagorantar jam’iyar.
Iliya ya ƙara da cewa akwai buƙatar bin tsare-tsare cigaban ƙasa na shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu.
Amma kuma wasu ƴan jam’iyar adawa sun nuna rashin jin daɗinsu na ka sauya sheƙar.
Kingsley Chinda shugaban marasa rinjaye ya ce kamata ya yi a yi watsi da sauya sheƙar saboda ɗan majalisar bai cika ka’idar da kundin tsarin mulki ya shinfida ba kafin sauya jam’iya.
Chinda ya ce kamata ya yi Iliya ya fara sauya jam’iya a matakin mazaɓarsa dake jihar Filato tukunna.