An samu ambaliyar ruwa a Adamawa

Anguwan Tana, al’ummar karamar hukumar Yola ta Arewa, sun shiga tasgaro a ranar Alhamis sakamakon ambaliya daga kogin Kilange da kogin Faro.

Mazaunan garin a babban birnin jihar yana kan gabar kogin Benue, wanda ya ratsa Yola.

Al’ummar sun koka da barnar da suka samu a gonakinsu biyo bayan ambaliyar ruwan.

Da ya ziyarci yankin da lamarin ya shafa a ranar Juma’a, Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa, ADSEMA, Dokta Mohammed Suleiman, ya ce da a ce mutane ba su yi kunnen-uwar-shegu da gargadin da aka yi musu ba, da haka bai faru ba.

Shugaban ADSEMA ya shaida wa manema labarai cewa, “Kafin a fara damina, lokacin da muka samu hasashen ambaliyar ruwa, mun gargade su.”

Yayin da yake jaddada bukatar suna bai wa gwamnati hadin kai a kodayaushe, ya ba su tabbacin samar da kayayyakin jin-ƙai.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...