An sallami ƴan sanda uku daga bakin aiki kan isan wani dalibi

Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta ce ta sallami jami’an ta uku da aka samu suna da hannu a kisan wani dalibin makarantar kimiya da Fasaha ta jihar.

A ranar 4 watan Satumba ne aka kashe dalibin mai suna,Quayum Ishola dake shekarar karatu ta biyu a fannin karatun difilomar fasahar wutar lantarki da kayan wuta.

Ishola wanda aka ce ya mutu a asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin  sanadiyar tsinkewar a jijiyarsa bayan da jini ya yi ta kawararar daga wurin.

Ɗalibai sun gudanar da zanga-zanga ya zuwa hedkwatar  rundunar ƴan sandan jihar Kwara inda suka buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar abokin karatun na su.

Ɗaliban sun yi iƙirarin cewa an harbe shi ne a wurin wani shingen binciken ababen hawa dake na ƴan sanda dake  kan titin Panat-Shoprite a Ilorin.

A ranar 9 ga watan Satumba, Oluwimiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya ya sanar da sunayen ƴan sandan dake da hannun a lamarin da suka haɗa da Abiodun Kayode (inspector), James Emmanuel (inspector), da kuma sajan Oni Philip  dukkansu daga sashen ayyukan yau da kullum na rundunar ƴan jihar.

A wata sanarwa ranar Juma’a, Adetoun Ejire-Adeyemi  mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kwara ya ce tuni aka tasa keyar ƴan sandan uku ya zuwa gidan yari.

More News

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da ƴan ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an ƴan sanda da kuma sojoji suna ɗaukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...

Sojoji sun kashe ɗan Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya na Birged Ta 21 dake aiki da rundunar Operationa Haɗin Kai dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso...