An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos bayan da ya dawo Najeriya daga ƙasar Amurka.

Sowore wanda ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce an sake shi bayan wasu ƴan mintoci.

Sowore wanda shi ne jagoran ƙungiyar nan ta #Revolutionnow dake kira da a gudanar da juyin juya hali a Najeriya ya ce jami’an hukumar lura da shige da fice ta Najeriya sun ƙwace masa fasfonsa na tafiye-tafiye bisa umarni da aka basu daga sama kamar yadda suka sheda masa.

Ya ce tsare shi da aka yi ba abu ne ba da baiyi tsammani ba saboda yadda gwamnatin kama karya ta  Bola Ahmad Tinubu ta faɗaɗa musgunawar da take wa masu adawa da ita.

More from this stream

Recomended