An saki dan jaridan Premium Times

[ad_1]

Dan jaridar premuim Times

Hakkin mallakar hoto
Premuim times

Image caption

An gurfanar da Ogundipe a gaban kotu ba tare da lauyansa ba a ranar Laraba

Kotu ta ba da belin dan jaridan kafar yada labarai ta Premium Times, Samuel Ogundipe, wanda jami’an ‘yan sanda suke tsare da shi tun ranar Talata.

Da safiyar ranar Juma’a ce aka saki, Mr Ogundipe bayan da alkalin kotun Abdulwahad Mohammed ya ba da belinsa a kan naira dubu dari biyar da gabatar da wani wanda zai tsaya masa wanda zai kasance mazaunin Abuja ne.

An sako dan jaridan ne bayan cika wadannan sharuddan na beli.

A ranar Laraba ne dan jaridar ya gurfana a gaban kotu ba tare da lauyansa ba.

A wannan ranar alkalin kotun ya amince da bukatar da rundunar ‘yan sanda ta shigar, inda ta nemi a ba ta damar ci gaba da tsare dan jaridar har zuwa ranar 20 ga watan Agusta.

Sai dai a zaman kotun na ranar Juma’a an bari lauyan dan jaridan ya shiga kotun, inda ya nemi kotun ta ba da belinsa.

Tun farko hukumar ‘yan sanda ta ce tana zargin Mista Ogudundipe ne da amfani da wasu bayannan sirri.

A cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin hukumar ‘yan sanda, Jimoh Moshood, ta yi zargin cewa matakin da dan jaridan ya dauka, abu ne da ya saba wa dokokin tsaro kuma zai iya ta da husuma.

Sai dai lauyan kamfanin Premuim Times, Iti Ogunye, ya ce babu adalci a cikin sanarwar da hukumar ‘yan sanda ta fitar.

Tun a ranar Talata ne ake tsare da dan jaridan saboda ya ki bayyana majiyar da ta ba shi bayani kan wani labari da ya rubuta.

Labarin wanda wasu kafofin yada labarai suka rubuta ya bayyana cewa Baban Sufeton ‘yan sanda Ibrahim Idris ya mika wani rahoto ga Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo.

Rahoton ya dora laifi ga shugaban hukumar tsaron farin kaya Lawal Daura, wanda da aka kora kan rawar da ya taka wajen tura jami’an tsaro zuwa majalisar dokokin kasar.

‘Yan Najeriya da kafofin watsa labarai na cikin gida da na waje da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’Adama irin su Amnesty International sun yi Allah-wadai da matakin.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...