An sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS.
An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙungiyar a wurin taron shugabannin kasashen karo 65 da aka gudanar a fadar Aso Rock dake Abuja.
A cikin watan Yulin shekarar 2023 aka fara zaɓen Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS a wani taron da aka gudanar a ƙasar Guinea-Bissau.
Tinubu shi ne shugaban Najeriya na 8 dake jagorantar ƙungiyar ta ECOWAS.
Sake zaɓen Tinubu na zuwa ne dai-dai lokacin da ƙungiyar ke fuskantar ƙalubalen juyin mulki a wasu ƙasashe mambobin ƙungiyar.