
Wata tankar man fetur dake makare da mai ta fadi akan titin Lambata-Lapai-Agaie dake jihar Niger inda hakan ya jefa tsoro da zullumi a zukatan mazauna yankin.
Jaridar Daily ta gano cewar tankar man ta taso ne daga birnin Lagos akan hanyarta ta zuwa Kano ta jirkice ta fadi da asubahin ranar Lahadi a kauyen Takalafiya dake karamar hukumar Lapai ta jihar Niger.
Wani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar ya faÉ—awa jaridar ta wayar tarho cewa inda lamarin ya faru na da tazarar kilomita 2 ne daga garin Lapai.’
Ya ce wurin da motar ta fadi na daga cikin wurin da kamfanin NNPCL ya gyara yan da suka wuce amma har titin ya fara lalacewa a yanzu. VhhbvCi jj,hjv
Shima Mohammed Hassan Sonmaji ya fadawa wakilin jaridar ta Daily Trust cewa daukik gaggawa da jami’an kashe gobara na jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida dake Lapai da kuma na jami’an hukumar NSCDC shi hana faruwar wata mummunar masifa.
Ya kara da cewa shugabannin kungiyar NUPENG shiyar Lapai sun garzaya ya zuwa wurin domin taimakawa wajen shawo kan lamarin.
Daga bisani an kwashe wani daga cikin man a cikin jarakuna domin rage asara da kuma kare gurbacewar muhalli.
We

