An sake kamo fursunoni 5 da suka tsere daga gidan yarin Kogi

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da sake kama mutane 5 daga cikin 12 da suka tsere daga gidan gyaran hali na Koton Karfe a jihar Kogi biyo bayan tserewar da suka yi da asubahin ranar Litinin.

Mutum guda daga cikin jami’an tsaron hukumar gidajen gyaran hali ne ya rasa ransa a lokacin da ɗaurarrun suke ƙoƙarin tserewa.

A cewar wata sanarwa da DCC Abubakar Umar mai magana da hukumar gidajen gyaran hali ta Najeriya ya fitar ya ce ɗaurarru sun tsere ne da tsakar daren ranar Litinin bayan da wasu suka lalata kwaɗon kofar wani sashe na gidan gyaran halin.

Sanarwar ta ce biyo bayan samun rahoton faruwar lamarin shugaban hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche ya haɗa kai da shuagabancin sauran hukumomin tsaro da kuma mai bawa gwamnan jihar Kogi shawara kan sha’anin tsaro inda suka gaggauta tura karin jami’an tsaro domin dawo da doka da oda da kuma killace gidan gyaran halin.

“Kawo yanzu an sake kamobbiyar daga cikin fursunonin a yayin da ake cigaba da bin diddigin sauran da suka tsere,” a cewar sanarwar.

More from this stream

Recomended