An sake gano gawar wani shugaban Fulani da ya ɓata a jihar Filato

An gano gawar wani Arɗon Fulani, Umar Ibrahim da ya ɓace a cikin wata rijiya dake kauyen Jokom a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar samar da tsaro a jihar Plateau ta Operation Safe Haven, Kaftin Oya James shi ne ya sanar da haka ga manema labarai.

Marigayin shi ne ke riƙe da sarautar Ciroman Kumbun dake gudumar Magun.

Shugaban kungiyar Gan Allah Fulani Development Association of Nigeria, (GAFDAN) Garba Abdullahi ya fadawa jaridar Daily Trust cewa marigayin ya ɓace bayan da ya bar asibiti domin ya sayowa matarsa da aka kwantar abinci.

“Bayan bincike na kwana huɗu an gano gawar a wata rijiya da ba a amfani da ita dake kusa da asibitin” a cewar Garba.

Shugaban ya shawarci mutanensu da su kwantar da hankali kuma kada su ɗauki doka a hannunsu.

More from this stream

Recomended