An rufe babbar gadar Lagos

[ad_1]

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsawon gadar ya kai kusan kilomita 12

Gwamnatin jihar Lagos da ke Najeriya ta ce za ta rufe babbar gadar nan mai muhimmanci da ta hada tsibirin Lagos da sauran unguwannin birnin domin binciken ko gadar na bukatar gyara.

Gadar wadda ake kira third Mainaland Bridge za a rufe ta ne na tsawon kwana hudu kamar yadda gwamnati ta yi alkawali.

Kwamishinan ayyuka na jihar Ade Akinsanya ya ce an tanadi jami’an kula da zirga-zirga a sauran hanyoyi domin saukake wa al’umma kai da komawa a birnin.

Gadar mai tsawon kusan kilomita 12 an kaddamar da ita ne a shekarar 19 90, lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Basamasi Babangida.

Ana kallon gadar a matsayin mai matukar muhimmanci a birnin na Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Matakin dai zai haifar da cushewar motoci a sauran hanyoyin da ma’aikata da ‘yan kasuwa za su bi domin isa cikin birnin na Lagos.

Cushewar hanyoyin kuma zai fi shafi ma’aikata da ‘yan kasuwa musamman lura da gadar ita hanya mafi sauki ta shiga birnin Lagos.

Wasu mazauna birnin Lagos sun shaida wa BBC cewa dole su sauya lokacin fita sabanin lokacin da suka saba fita saboda tsoron cushewar hanyoyin mota don kaucewa makara zuwa wurin aiki da kasuwa.

Wasu kuma sun ce rufe gadar zai sa masu zirga-zirgar motocin sufuri kara kudi ga fasinja saboda kewayen da za su yi da kuma cunkoso kafin shiga Ikko.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...