9.7 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaAn rage wa'adin shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Filato

An rage wa’adin shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Filato

Date:

Related stories

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Tinubu ya bada umarnin sakin yaran da aka gurfanar a gaban kotu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin ...
spot_imgspot_img

Majalisar dokokin jihar Filato ta rage wa’adin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a jihar daga shekara uku zuwa biyu.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Mr Matthew Kwarpo ya faɗawa manema labarai ranar Laraba a Jos cewa an rage wa’adin ne domin da cewa da gyaran dokar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Filato ta shekarar 2024.

Ya ce rage wa’adin ya dace da bawa ƙananan hukumomi ƴancin gashin kai da aka yi kwanan nan a Najeriya ya ƙara da cewa ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kanke daga jam’iyar APC, Joseph Gokum shi ne ya gabatar da kuɗirin neman gyarar dokar kananan hukumomi ta shekarar 2017.

Kwarpo ya ce sanya gajeren wa’adi zai bada damar samar da lokacin gwajin da za a auna  tasirin bawa ƙananan hukumomin yancin cin gashin kai.

Ya tabbatarwa da jama’ar jihar cewa an ɗauki matakin ne domin cigaban jihar ba wai dan biyan buƙatun wasu mutane ba.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories