An raba ƴan biyun da aka haifa manne da juna a Isra’ila

Yanzu haka ƴan biyun na ci gaba da murmurewa

Wasu jarirai mata biyu ƴan shekara guda da aka haifa da kai a manne, sun yi tozali da juna a karon farko tun bayan samun nasarar raba su da aka yi, a wata tiyata da ba kasafai aka saba yin irinta ba a Isra’ila.

An kwashe wata da watanni ana shirya yadda za a yi wannan gagarumin aiki da aka shafe awanni 12 ana yi a cibiyar lafiya ta Soroka da ke birnin Beersheba.

Ya samu halartar mayan likitoci daga ciki da wajen Isra’ilar.

A halin da ake ciki jariran da aka boye sunansu na ci gaba da murmurewa.

“Suna shan iska, har ma su ci su kuma sha da kansu ba tare da taimakon wata na’ura ba” kamar yadda Eldad Silberman, shugaban sashen tiyata na cibiyar lafiya ta Soroko ya shaida wa kafar watsa labaran Channel 12 ta Isra’ila.

Wannan ne karon farko da aka yi irin wannan aiki a Isra’ila, kuma karo na 20 da aka yi a duk duniya baki daya.

Watanni kafin wannan tiyata, an riƙa cusa wasu abubuwan rage raɗaɗi a cikin kawunansu.

Daga nan aka yi amfani da sabuwar fatar da aka shimfida a ɓangaren da aka raba, duba da cewa wajen a hade yake a baya, ba shi da tasa fatar.

Kafin tiyatar sai da aka ƙiƙiri nau’in halittar jariran su biyu, sannan aka yi gwaji, in ji Micky Gideon, wata babbar jami’a a Soroko, babban abin farin ciki shi ne komai ya tafi daidai.

More from this stream

Recomended