An nemi mata su yi yajin jima’i don bijire wa dokar zubar da ciki | BBC Hausa

Alyssa Milano addressing reporters

Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty

Image caption

Kiran da Alyssa Milano ta yi na shiga yajin jima’i ya jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta

Fitacciyar jarumar fina-finai a Hollywood kuma ‘yar fafutukar gangamin #NiMaHaka wato #MeToo Alyssa Milano ta bukaci mata su nuna bijirewarsu ta hanyar kauracewa maza don nuna adawa da sabuwar dokar zubar ciki a jihar Georgia.

“Matukar mata ba su samu ikon doka a kan jikkunan da suka mallaka ba, to ba za mu iya kasadar daukar ciki ba,” ta fada a shafinta na Twitter.

Georgia ita ce jiha ta baya-bayan nan a Amurka da ta kafa doka don takaita zubar da ciki.

Sakon na Twitter da jarumar ta wallafa ya janyo rarrabuwar kawuna a shafin sada zumunta, lamarin da ya haifar da wata muhawarar da ta sa taken #YajinJima’i ya karade Twitter a Amurka.

An tsara cewa dokar mai lakabin “bugun zuciya” da Gwamna Brian Kemp ya sanya wa hannu a ranar Talata, za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairu.

Me dokar ta kunsa kuma don me ta haddasa ce-ce-ku-ce?

Dokar ta haramta zubar da ciki da zarar an iya gane cewa zuciyar dan da ke ciki ta fara bugawa – abin da ke daukar tsawon kimanin mako shida na juna biyu.

Mata da dama ba sa sanin sun samu juna biyu idan ciki yana da mako shida, galibin mata sukan fara laulayi ne idan ciki ya kai kimanin mako tara.

Sai dai, ana sa ran cewa dokar za ta fuskanci kalubala a gaban kotuna.

Wani alkalin kotun tarayya ya tokare irin wannan doka a Kentucky bayan an tsara za ta fara aiki jim kadan, don kuwa tana iya cin karo da tsarin mulki, a lokaci guda kuma dokar hana zubar da ciki dan mako shida da jihar Mississippi ta zartar a watan Maris, kuma za ta fara aiki a watan Yuli, ita ma tana fuskantar kalubala.

JIhar Ohio ma ta taba zartar da irin wannan doka a shekarar 2016, amma gwamnan jihar ya ki amincewa da ita.

Yaya batun yajin jima’i’?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sakon Twitter na jaruma Alyssa Milano da ke kira ga mata su dauki mataki a ranar Asabar ya sanya nan da nan sunan tauraruwar da taken #SexStrike sun karade Twitter.

Mutane sama da 35,000 suka nuna cewa sakon twitter din ya burge su, kuma an sake tura sakon sau fiye da 12,000.

Wata takwarar aikin fim Bette Midler ta wallafa sakon twitter don nuna goyon bayan Misis Milano.

Sai dai kuma nan da nan sakon ya janyo martani a intanet, kama daga masu goyon bayan sabuwar dokar da kuma wadanda suka soki lamirin azancin cewa da jima’i ne kadai mata ke iya faranta ran maza.

“Na yaba wa niyyar yin haka, amma batun #yajinjima’i ba abu ne mai kyau ba kuma tunani ne na masu wariyar jinsi,” wata ta rubuta a Twitter.

Da take kare kanta, jaruma Alyssa daga bisani ta wallafa wani sharhi a twitter dangane da tasirin yajin jima’i, lamarin da ya sake janyo mata suka daga masu amfani da intanet.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum É—aya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe Æ´an ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faÉ—a tsakanin Æ´anbindiga da Æ´anbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...