An naɗa Damagum a matsayin sabon shugaban riko na jam’iyyar PDP

Kwamitin zartarwa na uwar jam’iyyar PDP ya sanar da naɗa Ilya Umar Damagum a matsayin sabon shugaban riko na jam’iyyar.

Kafin zama shugaban jam’iyyar Damagum ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyar arewa.

Debo Ologunagba mai magana da yawun jam’iyyar shi ne ya sanar da haka a Abuja.

Naɗin na Damagum na zuwa ne biyo bayan umarnin da wata kotu ta bayar da ya hana tsohon shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu daga ayyana kansa a matsayin shugaban ta.

More News

Ƴan fashin daji sun kashe ɗan sanda ɗaya a wani shingen bincike a Zamfara

Ƴan fashin dajin a ranar Lahadi sun kai da farmaki kan wani shingen binciken ƴan sanda inda suka kashe ɗan sanda guda ɗaya tare...

Babu ƙamshin gaskiya a batun fara dauƙar ma’aikatan Immigration

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce hukumar lura da shige da fice ta Najeriya a yanzu haka bata fara ɗaukar ma'aikata ba inda ta shawarci...

An bayyana dalilin da yasa ba a fara rabon kayan abincin da gwamnatin tarayya za ta raba ba

Fadar shugaban ƙasa ta ce ma'aikatar aikin gona da wadata ƙasa da abinci tana kan matakin karshe na fara sakin hatsi metric tan 42000 ...

Majalisar dokokin Zamfara ta tsige kakakinta saboda tsanantar rashin tsaro a jihar

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, tare da nada Bashar Gummi, a matsayin kakakin majalisar. Hakan ya biyo bayan kudirin da dan...