
Aloy Ejimakor lauyan Nnamdi Kanu ya ce an dauke shugaban kungiyar ta IPOB daga hannun DSS ya zuwa gidan gyaran hali dake jihar Sokoto biyo bayan yanke masa hukuncin kisa da aka yi.
“An dauke Mazi Nnamdi Kanu daga hannun hukumar DSS ya zuwa gidan gyaran hali dake Sokoto da ya yi nisa sosai da lauyoyinsa,iyalai, masoya da kuma masu yi masa fatan alkhairi,” lauyan ya rubuta a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
A ranar Alhamis ne mai shari’a, James Omotosho alkalin babbar kotun tarayya dake Abuja ya samu Kanu da aikata laifin ta’addanci.
An yanke masa hukuncin daurin rai da rai kan laifi na É—aya, huÉ—u, biyar da kuma na shida daga cikin laifuka 7 da ake tuhumarsa akai.
Da yake yanke hukuncin alkalin ya ce Kanu mutum ne da bai kamata a hada shi zama da mutane masu natsuwa ba saboda dan ta’adda ne na Æ™asa da Æ™asa.

