An lakaɗa wa fasto duka kan sukar shugaban ƙaramar hukuma

NIG POLICE

Hakkin mallakar hoto
NIG POLICE

Image caption

Yanzu haka dai Faston an garzaya asibiti da shi saboda raunikan da aka ji masa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane 10 wadanda take zargi da hannu wajen lakaɗawa wani Fasto dukan tsiya.

Cikin wata sanarwa da rundinar reshen jihar Ebonyi ta fitar ta ce Fasto Okochi Chuwu Obeni ya ga ta kansa ne saboda zargin da mutanen suka yi masa cewa ya caccaki shugaban wata karamar hukuma a shafin Facebook.

Sanarwa ta kara da cewa ciki wadanda ta kama har da Mista Julius Amadi Nyerere wanda shi ne ya jagoranci wannan aika-aika, kuma yanzu haka suna hannun rundunar inda take ci gaba da gudanar da bincike.

A cewar sanarwar binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, an ci zarafin Fasto Fasto Okochi Chuwu Obeni ne bayan da ya soki shugaban karamar hukumar Afikpo ta Arewa Ogbonnia Oko Enyim ta shafinsa na Facebook, game da rushe gidan sirikansa da wasu shaguna da kuma farfasa wata mota.

  • Wannan ne ya sanya Fasto Okochi Chuwu ya rubuta cewa duk in da aka yi abin da bai kamata ba, dole kowa yayi Allah-wa-dai dashi ba tare da la’akari da wanda abin zai ɓatawa rai ba, lamarin da ya harziƙa magoya bayan shugaban karamar hukumar har ta kai suka dauki doka a hannunsu.

    Wani hoton bidiyo da ke yawo a intanet ya nuna yadda matasan suka ɗaure hannun Fasto Okochi Chuwu Obeni ta baya, suka kwantar dashi, sannan suka dinga zafga masa bulala suna watsa masa ruwan kwata a kan idon jama’a, daga bisani kuma suka tilasta masa janye kalaman da yayi.

    Yanzu haka dai yana asibiti saboda raunikan da aka ji masa, kamar yadda sanarwar ta zayyana.

    Haka kuma fasto Okochi ta shafinsa na facebook din, ya yaba wa majalisar sarakunan yankin, saboda tilasta wa shugaban karamar hukumar ya biya tare da gyara abubuwan da ya sa aka lalata.

    To sai dai kuma bayan da jami’an tsaro suka ɗauki mataki kan batun ne, sai Fasto Okochi ya sake wani rubutun a facebook inda ya ce babu wanda yasa shi rubutun da ya kai ga yi masa dukan tsiya.

    Ya kuma ƙara da cewa ya yi ne kawai don neman samun kyakkyawan shugabanci da adalci a tsakanin al’ummar yankin.

    Ya yi zargin cewa abinda shugaban Afikpo ta Arewa ya aikata ya yi ne saboda yana ganin kalaman a matsayin wata barazana ga makomar kujerarsa.

    More News

    Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

    Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

    Ɗan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

    Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

    Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

    Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

    An kashe kwamandan soji a Katsina

    An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...