
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta sanar da karbar ƴan Najeriya 180 da aka dawo dasu gida daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X ta ce hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya IOM ce ta taimaka wajen dawo da mutanen gida.
Hukumar ta ce mutanen da aka kwaso an sauke su ne a birnin Kano a ranar Talata sun hada da maza 122, ƙananan yara maza 18, jarirai maza uku sai manyan mata 18 da kananan yara mata 5 da kuma jarirai mata huɗu.
NEMA ta bayyana wasu daga cikin mutanen sun nuna alamar suna ɗauke da cutar zazzaɓin cizon sauro da sauran ƙananan ciwuka kuma sun samu kulawa daga jami’an kiwon lafiya.