An kwaso ƴan Najeriya 180 daga ƙasar Libiya

Ofishin hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA a jihar Lagos ya ce sun karɓi ƴan Najeriya 180 da aka dawo da su gida daga ƙasar Libya.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X da ake kira da Twitter a baya ta ce waɗanda aka dawo da su gidan sun hada da mata 67, maza  55, ƙananan  yara 42 sai kuma jarirai 16.

NEMA ta ce mutanen sun iso filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos da misalin ƙarfe 07:30 na daren ranar Laraba a cikin jirgin saman kamfanin Al-buraq.

Mutanen sun samu nasarar dawowa gida da taimakon hukumar lura da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya baya da suka nuna sha’awarsu ta dawowa bisa raɗin kansu.

More News

TCN na ci gaba da ƙoƙarin gyaran wutar lantarkin da ta lalace kwana biyu

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da ci gaban da aka samu wajen farfado da rukunin wutar kasa bayan wata tangardar...

Magoya bayan jam’iyyar NNPP sun ƙona jar hula

Wasu daga cikin mambobin wani tsagi na jam'iyar NNPP sun barranta kansu da jagoran jam'iyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso inda suka riƙa...

PDP ta ɗauki hanyar warware rikicin jam’iyyar

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ce  an kawo karshen rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami'yar PDP. Mohammed wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin...

Dakarun Najeriya sun cafke wasu ƴan’aiken ƴanbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...