An kwace kofin Zakarun Afirka | BBC Hausa

'Yan wasan Esperance da kofin Zakarun Afirka

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Da farko an ba wa ‘yan Esperance nasara, aka mika musu kofin, to amma yanzu sai sun sake wasan karo na biyu

An umarci ‘yan kwallon kafar kungiyar Esperance ta Tunisiya da su mayar da kofin Zakarun Afirka da suka ci a makon da ya gabata, domin a sake wasa.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta yanke hukuncin cewa dole ne kungiyar ta sake maimaita wasanta na karshe na biyu, da Wydad Casablanca.

A fafatawarsu ta biyu a Tunisiya, ‘yan wasan kungiyar ta Moroko sun ki yarda su ci gaba da wasa har aka tashi saboda wata takaddama kan kwallon da suka ci aka hana.

Ita dai kungiyar Esperance ta Tunisiya ta yi canjaras ne a wasan karshen na karon farko da abokiyar karawar tata, Wydad Casablanca a can Moroko.

A karawarsu ta biyu ne a Tunisiya, Esperance din tana gaba a wasan da ci daya ba ko daya, sai bakin, ‘yan Wydad suka farke kwallon, to amma alkalin wasa ya hana.

Hakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Takaddama kan kwallon da ‘yan Wydad suka rama, lafiri ya hana

Wannan ne ya sa ‘yan kungiyar ta Moroko suka bukaci da lafirin da ya je ya duba na’urar hoton bidiyon da ke taimakawa wajen warware takaddama, domin, sanin gaskiyar lamarin.

To sai dai daga nan ne aka ce musu wannan na’ura ta VAR, da ke gefen fili, ba ta aiki, a kan hakan su kuma suka ce atafau, ba za su ci gaba da wasan ba.

Hakan ne kuma ya sa hukumomin wasan suka ayyana Esperance a matsayin wadda ta ci kofin na Zakarun Afirka, aka ba ta kofin.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Tun da farko ba a gaya wa ‘yan wasan na’urar VAR din ba ta aiki ba

Bayan nazari kan batun ne, a yanzu hukumar kwallon kafa ta Afirka ta bayar da umarnin a sake wasan, wannan karon kuma a wata kasa ‘yar ba-ruwanmu.

Sai dai kasancewar a yanzu ana dab da fara gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka, ba za a sake wannan wasa na karshe ba, har sai a karshen watan Yuli.

More from this stream

Recomended