Wata tawagar jami’an tsaro da ta ƙunshi sojoji da ƴan sanda da kuma ƴan bijilante sun ceto manoma 36 da ƴan fashin daji su ka yi garkuwa da su akan titin Marigayi/Bena dake ƙaramar hukumar Dankon/Wasagu ta jihar Kebbi.
A wata sanarwa da aka fitar mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Nasir Abubakar ya ce ƴan fashin dajin masu yawan gaske sun tare titin Marirai/Bena inda suka sace manoma 36 da ke dawowa daga gonakin su.
Ya ƙara da cewa tawagar jami’an tsaron haɗin gwiwa sun yi gaggawar isa wurin inda su ka yi musayar wuta da ƴan bindigar. Tawagar ta ci ƙarfin ƴan bingigar inda suka tsere cikin daji wasunsu na ɗauke da raunin harbin bindiga.
“An kuɓutar da manoman 36 ba tare da wani a cikinsu ya ji ciwo ba kuma tuni suka koma cikin iyali su,” a cewar sanarwar.