Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa an ceto 14 daga cikin daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Osara Okene da aka sace.
Idan ba a manta ba wasu ‘yan bindiga sun sace daliban ne da ke karatun jarabawar da za su yi ranar Alhamis da daddare.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun shigo cikin wajen, inda suka shiga dakunan karatu uku, sannan suka fara harbin iska don tsorata daliban.
Sai dai da manema labarai sun tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, William Ayata ta wayar tarho inda ya ce, “Ya zuwa yanzu an ceto 14 daga cikinsu, mutanen mu suna cikin daji suna kokarin gano sauran.”