An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo, a gaban kotu.

An mika hudu daga cikin sojojin da abin ya shafa ga ‘yan sanda yayin da biyu suka gudu. 

Sojojin hudu da aka kora sun hada da Sani Munzani mai shekaru 24;  Abubakar Auwalu, 26;  Abubakar Sani, 23 da  Muazu Hassan, 22. 

An samu labarin cewa sojojin sun kashe jami’in hukumar ta NDLEA ne a watan Maris din shekarar 2024 a lokacin da suka far wa jami’an NDLEA da suka tsayar da su a lokacin da suke bincike a mahadar Ramat da ke Bida.

FaÉ—an ya kai ga daba wa Chimetalo wuka a bayansa.

An kai jami’in zuwa FMC Bida inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa. 

Yayin da suke gudanar da bincike kan lamarin, jami’an ‘yan sandan da ke aiki da ‘A’ Division Bida sun gano bindigar jami’in a wani daji da ke kusa ba tare da gidan harsashi ba.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...