Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta ce ta kori ɗaya daga cikin jami’anta mai suna Insifekta Michael Odey da ke da hannu wajen karbar kudi a hannun wani.
Hakazalika, ta bayyana cewa an gurfanar da wasu jami’an biyu da ke da hannu a wannan aika-aika tare da ba da shawarar a kore su kamar yadda aka tsara.
A Najeriya an dai saba ganin irin wannan tsakanin jami’an ƴan sanda, wato karɓar kuɗi a hannun mutane.
Wannan irin halayyar ta karɓar ba bisa ka’ida ba na daya daga cikin abubuwan da haddasa zanga-zangar #EndSARS wacce ta jawo hasara sosai.