Wasu mutane da kawo yanzu ba a san ko su waye ba sun kashe, Bala Tsoho Musa shugaban makarantar Abuja Rehabilitation Centre.
Musa wanda aka fi sani da Kwamared an gano gawarsa ne ranar Juma’a da daddare a cikin makarantar dake Kuchiko a ƙaramar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Hukumar Birnin Tarayya Abuja FCTA ita ta samar da makarantar domin koya sana’o’i ga almajirai da kuma sauran jama’a da aka kama suna gagari a birnin.
Wata majiya ta faɗawa jaridar cewa an gano gawar marigayin ne tare da kekensa na guragu.
Wata ƙarin majiyar ta bayyana cewa akwai katako a gefe da aka yi ittifakin da shi aka yi amfani wajen aikata kisan a yayin da ba aga dukkanin wayoyinsa biyu ba. Wata ɗaliba kurmar daliɓa dake yi musu aikace-aikace a gidansa ce ta ci karo da gawarsa lokacin da take kan hanyar komawa ɗakin kwanan dalibai daga gidan.
Da aka tuntubi DPO ɗin ƴan sandan dake lura da Bwari, DSP Babayola Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin.