An kashe mutum 19 a Borno’

[ad_1]

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Boko Haram na ci gaba da zama barazana a Najeriya

Akalla mutum 19 rahotanni suka ce an kashe a wani kazamin hari da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Mailari da ke cikin jihar Borno yankin arewa maso gabashin Najeriya.

An kai harin ne a Mailari da ke yankin Guzamala, kuma ana kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kai harin ranar lahadi da safe.

Rahotannin sun ce harin wanda aka kai ranar lahadi, ya tursasa wa daruruwan mutanen kayukan da ke yankin yin gudun hijira zuwa garin Munguno da suke makwabtaka.

Wani mazauni yankin da ya tsira daga harin ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ya kirga gawawwakin mutane 19 da aka kashe cikinsu har da dan uwansa inda kuma ya ce an yi wa wasu da dama yankan rago.

Sai dai ya ce ba zai iya tantance ko ‘yan Boko Haram ne suka kai harin ba.

Baya ga kisan mutane kuma, rahotanni sun ce maharan sun bude wuta tare da kone gidaje da satar abincin mutane bayan sun shiga kauyen a ranar Asabar da dare.

Hare-haren da ake kai wa a baya-baya nan a yankin arewa maso gabashi, wani babban kalubale ne ga jami’an tsaron Najeriya da ke ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram.

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...