An kashe mutane da dama a rikicin masarauta a jihar Ogun

Rikici ya barke a garin Ese-Oke  dake ƙaramar hukumar Obokun ta jihar Osun biyo bayan nadin basaraken gargajiya na garin da gwamnatin jihar ta yi.

Tashin rikicin ya fara ne bayan da gwamnatin jihar ta sanar da Timileyin Ajayi a matsayin Olojudo na Ido Ayegunle.

Amma kuma mazauna garin sun yi watsi da naɗin inda suka ce kamata yayi a ɗaga darajar hakimin garinsu ya zuwa matsayin.

Har ila yau sun yi ikirarin cewa Ajayi wanda suke zargin cewa  ya fito ne daga Ilesa bai cancanci ya mulke su tun da suna ƙarƙashin Ese-Oke.

Rikicin ya yi ƙamari a ranar Litinin lokacin da wasu mutane ɗauke da bindigogi suka shiga garin suka buɗe wuta suka jikkata mutane tare da kashe wasu.

Mutane da dama aka rawaito sun mutu a yayin da wasu da dama suka jikkata hotunan da aka riƙa yaɗawa a soshiyal midiya sun nuna yadda wasu mutane sanye da baƙaƙen kaya ɗauke da bindiga suna sauka daga mota ƙirar Toyota Hummer abun ya ƙara fargabar ƙarin samun rikici.

More from this stream

Recomended