An kashe mutane 6 wasu biyu sun jikkata a yayin da yan bindiga suka buɗe wuta a tashar mota a Kwara

Ƴan bindiga sun kashe mutane uku tare da jikkata wasu a wani mummunan hari da suka kai tashar mota dake Ilesha Ibaruba a ƙaramar hukumar Baruten ta jihar Kwara.

A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi kusan ƴan bindiga 10 ne suka isa yankin da maraicen  ranar Litinin inda suka bude wuta kan wasu mutane dake hutawa a wata mashaya.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun dira a gurin ba tsato ba tsammani inda suka fara harbin kan me uwa da wabi abun da haifar da tsoro da kuma rudani.

Daga bisani jami’an tsaro sun isa wurin inda suka ɗauke gawarwakinsu ya zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Ilesha Ibaruba kana suka garzaya da waɗanda suka jikkata asibiti.

Da yake tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin Adetoun Ejire- Adeyemi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin.

More from this stream

Recomended