
Aƙalla Mutane 25 aka kashe a hari na baya-bayan nan da aka kai kan wasu al’ummomi dake jihar Filato.
An kashe mutanen ne lokacin da wasu ƴan bindiga suka farma ƙauyen Kimakpa dake gundumar Miangu a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar da karfe 02:45 na daren ranar Litinin.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi mazauna garin ne suka ankarar da jami’an tsaro abun da ya jawo kai ɗaukin gaggawa daga jami’an sojoji, ƴan sanda da kuma yan sandan kwantar da tarzoma da aka ajiye a Miangu.
Jami’an tsaron sun yi musayar wuta da maharan abun da ya rage girman ɓarnar harin.
An gano gawarwakin mutane 25 a binciken da aka yi a yayin da aka garzaya da wasu mutane huɗu da suka jikkata asibiti.
Sojoji sun kaddamar da farautar maharan a yayin da aka tura karin jami’an tsaro ya zuwa yankin.