
Akalla mutane 17 aka rawaito wasu da ake zargi mayakan kabilar Jukun ne su ka kashe bayan da suka kai wani tsararren farmaki kan wani s yan gudun hijira dake dawowa gidajensu a kauyen Tse Ajogo dake karamar hukumar Wukari ta jihar Taraba.
Akalla wasu mutane 10 ne suka jikkata a harin da aka kai ranar 10 ga watan Disamba A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’ani tsaro
Ya ce maharan sun kai farmaki kan kauyen da misalin karfe 06:00 na asuba inda suka rika harbin kan me uwa da wabi kan mazauna kauyen dama yan kuma gudun hijira inda ya kara a cewa wasu mutane da dama babu masaniyar inda suke a yayin da aka ƙona gidaje 7 a harin.
Makama ya ruwaito wata majiya dake da masaniya kan harin na cewa wannan ne karo na biyu da ake kai farmaki makamancin haka a kan yan gudun hijirar dake komawa gidajensu.
Kauyen na da nisan akalla kilomita 3 daga garin Rafin Kada inda yake da sauki kai hari.
Kawo yanzu dai rundunar yan sandan jihar Taraba bata fitar da wata sanarwa ba kan harin.

