Mambobin ƙungiyar ƴan uwa musulmi ta Najeriya da aka fi sani da ƴan Shi’a sunyi arangama da jami’an ƴan sanda a birnin tarayya Abuja.
An yi arangamar ne a yankin Wuse dake birnin lokacin da ƴan ƙungiyar suke gudanar jerin gwanon tattaki na ranar Arba’een.
A wata sanarwa, Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja tayi iƙirarin cewa mambobin ƙungiyar sun kai farmaki tare da kashe ƴan biyu.
Mai magana da yawun rundunar ta ƙara da cewa an garzaya da jami’an ƴan sanda biyu zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.
Ta ƙara da cewa an kama wasu mutane a yayin arangamar kuma tuni al’amura suka cigaba da gudana a birnin kamar yadda aka saba.
Sai dai a wata sanarwa da ƙungiyar Shi’a ta fitar mai magana da yawunta Sidi Mainasara yayin zargin cewa ƴan sanda sun kashe mambobin ƙungiyar da dama .