An kammala aikin jigilar alhazan bana

[ad_1]








Hukumar Aikin Hajji Ta Ƙasa, NAHCON, ta kammala aikin kwashe mahajjatan bana a daren ranar Juma’a.

Alhazan da suka hada da yan jirgin yawo da kuma jami’an hukumar ta NAHCON sun tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Da yake magana da manema labarai, kwamishina a hukumar dake lura da aiyuka, Abdullahi Modibbo ya ce hukumomin alhazai na jihohi sun yi rijistar maniyyata 40,000 ya yin da kusan maniyata 19,000 ne suka yi rijista ta kamfanonin shirya tafiye-tafiye.

Amma Modibbo ya ce jinkiri da aka samu wajen kammala jigilar alhazan ya faru ne sakamakon rashin kammala rijistar mahajjata da wuri ya karfafa cewa NAHCON ta yi kokari sosai wajen ganin an kammala aikin akan lokaci.

“Alhazai basu fito rijistar ba akan lokaci idan da sun fito a lokacin da ya dace to da za a kammala komai da wuri kafin yanzu,” ya ce.

Modibbo ya kara da cewa na sa ran fara kwaso alhazan ranar 27 ga watan Agusta.




[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...